728 x 90

An fara kada ƙuri’a a zaben ƙasar Kamaru

An fara kada ƙuri’a a zaben ƙasar Kamaru

Masu zaɓe miliyan 8 sun fara kaɗa ƙuri’a a zaɓen Kamaru Yau ne ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Kamaru, inda ‘yantakara 10 za su fafata a tsakaninsu, waɗanda suka haɗa da Paul Biya mai shekara 92. Mista Biya ya kwashe shekara 43 uku a kan karagar mulki kuma yanzu yana neman wa’adin mulki

Masu zaɓe miliyan 8 sun fara kaɗa ƙuri’a a zaɓen Kamaru

Zaɓen Kamaru

Yau ne ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Kamaru, inda ‘yantakara 10 za su fafata a tsakaninsu, waɗanda suka haɗa da Paul Biya mai shekara 92.

Mista Biya ya kwashe shekara 43 uku a kan karagar mulki kuma yanzu yana neman wa’adin mulki na takwas.

Akwai kuma wasu ‘yantakara kamar Issa Tchiroma Bakary, da Bello Bouba Maigari, da Madame Tomaino Ndam Njoya, da sauransu.

Sama da mutum miliyan takwas ne za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen, wanda ake yi wa kallon shi ne makomar matasan ƙasar saboda su ne mafiya rinjaye a al’ummar ƙasar.

Rashin aikin yi tsakanin matasan ƙasar ya zama muhimmin batu a wannan zaɓe, amma kusan duka ‘yantakarar sun yi alƙawarin shawo kan matsalar idan aka zaɓe su.

Zaɓen Kamaru
Zaɓen Kamaru

admin
ADMINISTRATOR
PROFILE

Posts Carousel

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked with *