728 x 90

Binnewa a teku, da sauran abubuwan da ba ku sani ba game da Osama bin Laden

Binnewa a teku, da sauran abubuwan da ba ku sani ba game da Osama bin Laden

Kimanin shekara 24 ke nan bayan ɗaya daga cikin hare-haren ta’addanci da ya girgiza duniya, inda ƴan ƙungiyar al-Qaeda suka ƙwace iko da jiragen fasinja, kuma suka yi amfani da su wajen kai hari kan muhimman wurare a Amurka. Amurka ta zargi Osama bin Laden da bayar da umarnin kai harin na ranar 11 ga

Kimanin shekara 24 ke nan bayan ɗaya daga cikin hare-haren ta’addanci da ya girgiza duniya, inda ƴan ƙungiyar al-Qaeda suka ƙwace iko da jiragen fasinja, kuma suka yi amfani da su wajen kai hari kan muhimman wurare a Amurka.

Amurka ta zargi Osama bin Laden da bayar da umarnin kai harin na ranar 11 ga watan Satumban 2011 a biranen New York da kuma Washington. Harin ya haifar da kashe kimanin mutum 3,000.

An kashe Osama bin Laden, mai shekara 54 a duniya ne lokacin da yake a matsayi na ɗaya cikin jerin mutanen da Amurka ke nema ruwa a jallo a duk faɗin duniya.

Bin Laden ya shafe kusan shekara 10 yana wasan ɓuya da dakarun Amurka, duk kuwa da ladar dala miliyan 25 da aka alƙawurta wa duk wanda ya taimaka wajen gano inda yake.

Wane ne Bin Laden?

An haifi Osama ne a ƙasar Saudiyya, kuma shi ne ɗa na 17 cikin ƴayan Mohammed bin Laden 52, wani attajirin ɗan kwangila a ƙasar ta Saudiyya.

Rasuwar mahaifinsa a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a shekarar 1968 ta sa ya zamo mai dimbin dukiya wadda aka yi ƙiyasin ta kai ta miliyoyin daloli.

Ya karanci ilimin injiniya a Jami’ar Sarki Abdulaziz da ke birnin Jeddah.

A shekarar 1998, Osama bin Laden ya bayar da wata fatawa a madadin ƙungiyar ‘Global Front for Jihad game da Yahudawa, inda ya ce kashe Amurkawa da ƙawayensu aiki ne da ya rataya kan Musulmai.

Iyalin Osama bin Laden

Bayanai sun nuna cewa Osama bin Laden ya kasance mutum ne mai yawan ƴaƴa mata da maza, sai dai ba a ƙididdige adadin ƴaƴan nasa ba, kuma ya auri mata da dama.

Sai dai an san Hamza, ɗa ga Osama, wanda aka saki wata murya tasa da aka naɗa a shekarar 2015, inda ya yi alƙawarin ɗaukar fansar kisan mahaifinsa sannan kuma ya gabatar da kansa a matsayin magajin mahaifinsa.

Sai dai bai daɗe ba aka kashe shi ta hanyar wani hari ta sama, a shekara ta 2019 lokacin mulkin farko na shugaban Amurka Donald Trump.

Omar ne ɗan Osama bin Laden na huɗu, kuma ya guje wa mahaifinsa a shekarar 2000, bayan ya ƙi kammala karɓar horo a wani sansanin masu iƙirarin jihadi a Afghanistan.

Akwai kuma ɗansa Sa’ad wanda wani harin Amurka ya hallaka a 2009 a ƙasar Pakistan.

Sai kuma Khalid, wanda aka kashe tare da mahaifinsa a harin da Amurka ta kai a gidansa a shekara ta 2011.

An yanka ta tashi

A ranar 19 ga Satumban 2001, kwana takwas bayan harin 11 ga Satumba da aka kai a Amurka, Amurkar ta zaci ta kashe Osama Bin Ladin yayin da yake ɓoye a tsaunukan Tora Bora na ƙasar Afghanistan.

Amma bayan wata shida, wato a ranar 18 ga Afrilun 2002, sai ya bayyana cikin ƙoshin lafiya.

Sai dai Amurka ta samu nasarar kama mutumin da aka zarga da kitsa harin 11 ga Satumba, Khalid Sheikh Mohammed.

Gwamnatin Amurka ta gina wani wurin ajiye masu laifi da ake kira Guntanamo Bay a ƙasar Cuba.

Me ya sa a Guantanamo ba Amurka ba? Maƙasudin hakan shi ne tuhumar fursunoni ba tare da laʼakari da dokokin Amurka ba.

Saboda suna son yin azaba gare shi yayin tuhumar, kuma ba za su iya yin hakan ba a ƙasar Amurka.

Yadda aka kashe Osama

A ranar 1 ga watan Mayun 2011, da kimanin ƙarfe 11:30 na dare ne shugaban Amurka na wancan lokaci Barrack Obama ya sanar da kisan Osama Bin Laden

An kashe Bin Laden ne a wani gida da ke birnin Abbottabad na ƙasar Pakistan bayan dogon lokaci na tattarawa da sarrafa bayanan sirri.

Gidan da aka kashe shugaban na AlQaeda ya kasance yana da tsaron da ba a saba gani ba: Katanga mai tsayi da wayar tsaro, tagogi marasa haske, da kuma rashin intanet da sabis ɗin waya. Ana ƙona duk wata sharar da aka samu a cikin gidan.

Girma da kuma tsarin gidan ya bai wa hukumomin Amurka mamaki.

Gidan na zagaye ne da wata katanga mai tsawon mita huɗu zuwa shida, kuma g

gidan ya nunka gidajen da ke makwaftaka da shi wajen girma sau takwas, sai dai babu tarho kuma babu intanet.

Wani abu da aka lura da shi shi ne mazauna gidan ba su da wani aikin yi ko kuma hanyar samun kuɗin da zai sa su mallaki ƙaton gida kamar wannan.

Wannan na ɗaya daga cikin abubuwan da suka ƙara janyo hankalin jami’ai a kan gidan.

To amma wani abu shi ne Osama bai taɓa fita daga gidan ba, saboda haka dole ne Amurkawan su san dabarar da za su gano wanda ke cikin gidan.

Yayin da suke bincike da sanya ido kan gidan, sai suka lura da wani mutum yana safa da marwa a lambun gidan, inda suka yi zargin Osama bin Laden ne.

Daga nan sai suka auna girmar inuwarsa.

Sun kira wani ɗan jarida mai suna John Miller, wanda ya taɓa yin hira da Osama a shekarun 1990, inda suka buƙace shi da ya ba su bidiyoyin da ya ɗauka na Osama yana tafiya domin kwatantawa da hotunan da suke da su na mutumin da suka gani yana zirga-zirga a gidan.

Kamanceceniyar ta yi yawa.

Ba kawai inuwar ba, har ma da ɗan ɗingishin da Osama yake yi ya zo daidai da abin da aka gani a bidiyon.

Haka nan wani abu da ya haifar da zargi shi ne yawan kayan da aka shanya a saman gidan, wanda ke nuna cewa akwai mutane da yawa da ke rayuwa a gidan.

Daga nan ne a ranar Lahadi, ƙwararrun dakarun Amurka daga rundunar Navy Seal Team Six ta ƙaddamar da samame a gidan a birnin Abbottabad, mai nisan kilomita 100 daga birnin Islamabad.

Shugaba Obama ya ce “babu wani ba’amurke da aka cutar” a lokacin samamen.

Wani jami’in Amurka da ya yi ƙarin haske kan harin ya ce sojojin sun kwashe kimanin minti 40 lokacin samamen.

Haka nan wani babban jami’in na Amurka ya ce ba tsegunta wa kowace ƙasa bayanan sirrin da aka tattara ba gabanin samamen, ciki kuwa har da ƙasar Pakistan.

“Mutane ƙalilan ne daga cikin gwamnatinmu suka san da samamen kafin a ƙaddamar da shi,” in ji jami’in.

Yadda aka binne Osama

Osama

An binne Osama bin Laden ne a cikin Tekun Indiya.

Shugaba Obama ya sanar cewa dakarun Amurka sun samu nasarar ɗaukar gawar Osama ne bayan “musayar wuta”.

Inda daga bisani gwajin halittar gado ya tabbatar da cewa lallai Osama ne aka kashe.

Jami’an ma’aikatar tsaro ta Pentagon sun ce an binne Osama ne a teku ne bayan yi masa sallah a kan wani jirgin ɗaukar jiragen yaƙi na Amurka.

Dalilin yin hakan, kamar yadda shugaban hukumar hukumar tattara bayanan sirri na Amurka a wancan lokaci Leon Panetta ya bayyana shi ne domin kada a binne shi a doron ƙasa, kabarinsa ya zama tamkar wajen bauta.

admin
ADMINISTRATOR
PROFILE

Posts Carousel

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked with *